Sunday, October 12, 2008

MAKAUNIYA: Waka


Daga
Ado Ahmad Gidan Dabino
E-Mail: gidandabino@yahoo.com


1. Allah gwani kai ne ka kagi samaniya,
Kai yo maza mata cikin su halitta.

2. Ka ce mu so Manzo Rasulu abin biya,
Da gun Aminatu Sidi ya cancanta.

3. Na san akwai so gaskiya ne ’yan’uwa,
Domin ko Rabbi ya sa shi nan ga halitta.

4. Me sa mutum ya zamo kamar wani jarumi,
Me ji kamar zai doke dukka halitta.

5. Da can ina zargi a kan mai so ku ji,
Na mai da shi wawa cikinsu halitta.

6.Yau ga shi na fada a tarko har wuya,
Bege a kan wata ’ya cikinsu halitta.

7. Kullum na zo barci in ta tararradi,
Domin tunanina yana a gare ta.

8. In don mafarki na yi sau zambar dubu,
Domin yawan shaukin in sami ganinta.

9. A cikin mafarki mun hade mun daddale,
Amma a fili babu wanda ya furta.

10. Kwayar idonta kawai tana rikitar da ni,
Balle ta yo farfar da na dube ta.

11. In tai fishi sannan take dada kyan gani,
Balle harara ta fi kyau a wurin ta.

12. Tsari da suffa ba batunsu a nan wurin,
Ta zarce duk wani kyau da za a musalta.

13. Hakuri damo ya sallama mata kun jiya,
A cikinsu mata ban ga wadda ta kai ta.

14. Ni na zamo sarki a harkar so ku san,
Amma a yau na zam mariri gun ta.

15. Ya zan yi ne na zamo gwani a wajen ta ni?
Har ma ta san ni ta san ina kaunarta.

16. Ni ba ni so na fada da baki ta san ina,
Mutukar masifar so yana a gare ta.

17. Babbar bukatata a ce ta san da ni,
Ta gane lallai ni ina begenta.

18. Ko da ko ba ta so gare ni ku tabbata,
Na cim ma burina a kan kaunarta.

19. Ya ’yan’uwa ku taho da tanyon agaji,
Ko na ji sau}i kan batun matsayinta.

20. Ya zan yi ne in warke ciwon nan kuwa,
In sami yarjewa cikin kalbinta.

21. Ciwo kadan da kadan yake dada karuwa,
Wata ran a wayi gari ya kai ka ka kwanta.

22. Ni shawara na bida gare ku mawallafa,
In bayyana ne ko ko kadda na furta.

23. ’Yan Dandali ku fito da amsar tambaya,
Ku malamai ne kan sa so ku fahimta.

24. In kun gaza kun ba mu kunya bai daya,
Sai dai na ce kaico a harkar son ta

No comments: