Tuesday, December 16, 2008SIRADIN RUBUTU

Daga

Nurudden Ado Gezawa salmannhur@yahoo.com
07028821493, 08077879218

Kamar yadda zukar kahon wanzamai kan zuko kwantaccen jini, haka yanayin da na kasance ciki na karance-karancen kirkira ya zuko kwantacciyar basirar kirkirar labarai a kwakwalwata. Basirar kirkirar da ta bani damar shusshuka irirrikan labaran da yabanyarsu ke kan ganiyarta ta habaka, wanda hakan ya sanyani zumudin yadda zan yi wajen sharer fagen samun karbuwar labaraina.
Kodayake dai furfura ta rinjayi baker suma a kaina amma ba ta tsufa ba ce, ballantana a ki jinjinawa hangen nesan da na yi wajen samarwa kaina suna na musamman a fagen rubuce-rubucen kirkira. Ba kuma zabar Kanon da na yi a matsayin garin da zai zamo sabon matsugunina, kasancewarta jigon hausa, ne abin jinjinawar ba, a’a, tunanin sifar da ta kyautu in je Kanon da ita ne.
Na sha jin ana cewa idan har kanawa na da rauni to bai huce na tsantsar kaunar Musulunci ba. Ko da yake dai ni ban yarda da wannan a matsayin rauni ba, illa iyaka dai mashigar da idan mutum kadangare ne to zai iya shiga bangon kanawa ta cikinta. Don kuwa, mutumin duk da kanawa suka lura mabiyin Allah ne kuma masoyin Manzon Allah ne, to take su ke karbarsa ba tare da bincikar ainihin hali ko asalinsa ba. Wannan ya sanya na tanadarwa kaina lakabi na musamman d azan shiga Kano da shi, wanda na tabbatar kanawa za su rinka kira na da shi cikin nishadi da karamci, wanda hakan n eke nuni da samun karbuwa gurin na kanawa. Matukar haka ta faru kuwa, to babu ko tantama zan cimma burina na samun karbuwa a ilahirin kasar Hausa.
A wata ranar lahdin farkon wani watan miladiyya da hantsi na shigo birnin na Kano cikin wata shudiyar baksuwajata, wadda na lilliketa da lakabin da na tanadarwa kan nawa, na biyo ta titin Gwarzo. Da yake ban san inda zan bi don zuwa dakin karatun Murtala Muhammed ba, inda nan ne ake taron kalubalen kungiyar marubuta rishen jihar Kano, sai na dakata a wani guri, da a gaba, zan san sunansa a matsayin Sabon-titi don yin tambaya. Tun kafin ma na fita daga motar mutane suka rinka tunkaro motar a guje, suna yin kabbara. Raina ya yi fari bisa ga zaton da na yin a cewa na shigo da kafar dama fiye da yadda na zata.
Amma ba haka al’amarin ya tafi ba, don kuwa mutanen na karasowa sai suka rinka lalubar makamai suna jibgar motar tawa. Kafin ma na ankara sun rotes gilasan motar, sun zaro ni daga cikin motar sun kuma fara yi mini rajamu.
Lokaci na gaba da na farfado sai na tsinci kaina cikin bandeji, a gurin dab a tare da bata lokaci ba na shaida asibiti ne. Haka na yi ta fama har zuwa lokacin da ma’aikaciyar jinyar ta lura dani, inda bad a jimawa ba babban likita, tare da wasu mutane suka zo gare ni.. Bayan da likitan ya duba jikina sai ya waiwayi daya daga cikin mutanen, wanda kayan dake jikinsa ke nuni da cewa shi dansanda ne, ya ce masa ‘Bismillah’
Dansandan ya yi mini wasu tambayoyi, na kuma amsa masa. Tambayar da ta fi bani mamaki ita ce wadda ya ce “Da ka san Kanon garin Musulmai ne mai ya sanya ka yi wa Musuluncin wargi?”
Kaina ya daure “Yi wa Musulunci wargi? Ban gane ba.”
Ya ce “To mai ka rurrubuta a jikin motarka?”
Na ce “Lakabin da na ke son mutanen Kano su sanni da shi.”
Ya dan nazarce ni kafin ya ce, “Za ka iya gaya mini lakabin da kake son Kanawan su sanka da shin?”
“Kwarai kuwa,” na shaida masa, “Ba wanda ya gagari Allah.”
Dansandan ya karangai da kai cikin jimami, “To ai kai ba haka ka rubuta ba. Abin da ka rubuta shine Bawan da ya gagari Allah.”
Sai a sannan na gane dalilin dukan da aka yi mini, wanda ya faru ta sanadiyyar rashin bin ka’idojin rubutu! Hakika na rubuta ‘Bawan da’ a maimakon ‘Ba wanda’ wanda hakan ya jirkita manufata. Lallai ka’idojin rubutu su ne siradinsa, kuma rashin binsu kan iya janyowa mutum rasa, ko da, ransa. Don haka wajibi ne bayan basirar rubutu ga marubuci, ya kyautu ya sani ya kuma kiyaye dokokin rubutu cikin rubutunsa.

Monday, October 13, 2008

SHAN RUWANA: Gajeren Labari


Daga
Muhammad Mahammad Assadiq
assadiqalwayz@yahoo.co.nz


Da gudu na shigo cikin gidan saboda tsannanin wahalar da Azumin yake ba ni. Ina shigowa sai na taras da su sun hada kayan shan ruwa tsibi-tsibi sai kawai na kama wata Kankana da gwaguya sai da na ga babu komai sai bawon fari fat da shi, duk na gaygaye ta kamar yadda biri yake yi.


Can kuma sai na sake hararar wani kwano da yake dauke da wani abu wanda ni kaina ban san ko mene ne ba, sai kawai na dauko na jefa a bakina, haba da dadi ya debe ni sai da na lumshe idanuna.


Haka na yi ta yi su kuma suna kallona suna dariya, ban daina ciye-ciyen ba sai da na ji cikina ya yi bam, sannan sai na kalli matan nawa da zummar in yi musu godiya, abin mamaki sai kawai ganin surakaina na yi a zaune a wajen.


Ashe matan nawa ne suka gayyato su shan ruwa, sumui-sumui sai kawai na shige cikin daki, sai da na bata wajen minti goma sannan daga ciki sai na ce “INA WUNINKU UMMA...”


Sai kawai suka fashe da dariya gaba dayansu...BA TA IYA GIRKI BA

Muhammad Mahammad Assadiq
assadiqalwayz@yahoo.co.nz

Kullum ni nake girka mana abincin da muke ci, saboda tsananin son ta da nake yi, ga shi kuma muna tsakiyar cin amarcinmu. A haka muka zauna har tsawon kwana ashirin da takwas na hutuna, na karshen shekara.


Da yamma na dawo daga wajen aiki bayan hutun nawa ya kare, ina shigowa sai na taras da ita a zaune ta takure a waje daya, sai na tambaye ta me yake faruwa, kun san abin da ta ce min?


"Yunwa nake ji" shi ne abin da ya fito daga bakinta, ni kuma sai na ce “Lafiya ba ki yi girki ba?”. Sai ta ce wai ita ba ta iya girki ba sai dai ni in dafa mana, abin ya bani haushi wanda har hakan ta sa na kasa cewa komai. Ni kaina yunwar ce ta koro ni gidan, dole na zage na yi mana abinci muka ci, har tana SANTI, tana ba ni labaran shirme don dadin abinci. Haka muka zauna kullum sai na yi mata abincin da za ta ci da rana sannan in fice. Na koya mata amma abin ina idan ta hada maka wani abincin ko Gidan Dabino da Dan Fagge ba za su iya ci ba.

Rannan sai kawai na dawo Break wanda kuma ba al'ada ta ba ce dawowa da rana.

Ina shigowa cikin gidan sai na ji wani Kamshi yana tasowa, da sauri na waiwaya a zatona wani ne yake biye da ni da abinci mai dadin kamshi haka, sai na ga babu kowa, na wuce cikin gidan na duba ban gan ta ba sai na yi tunanin tana Toilet ne, can sai na jiwo motsi a cikin dakin girki, abin mamaki, lekawar da zan yi sai na hango ta tana girki har da rawa, da na lura da kunnen ta sai na ga irin 'yar karamar rikoda ce a makale a kunnen tana shan KIDA. Zuwa na yi ta baya na dan taba ta, juyowar da za ta yi sai ta gan ni a tsaye KIKAM, sai ta kashe rikodar sannan ta ce sannu da zuwa, ban amsa mata ba sai na wuce kai tsaye na buda tukunyar, ga mamakina abincin ne yake wannan kamshin da na jiwo.

"Waye yake dafa wannan abincin?" Na tambaye ta, "Ni ce" Ta ba ni amsa kai tsaye. Sai kawai na dan debo na dandana, ba irin abincin da take CAKUDA mini ba ne maras dadi, kusan ma wannan ina iya cewa da kadan nawa ya dan dara shi dadi.Ga mamakina sai na ji ta katse ni da cewa, “Ni abincina ne ba na so ka ci shi ya sa na ce maka ban iya ba, wannan din ma ba za ka ci ba rabon ka shi ne kawai wanda ka dandana, sai dai ka dafa naka. Kai ka taba ganin macen da ba ta iya girki ba?”.Haushi da ya kama ni sai kawai na SUNGUME tukunyar abincin na yi waje a guje!.

Sunday, October 12, 2008

MAKAUNIYA: Waka


Daga
Ado Ahmad Gidan Dabino
E-Mail: gidandabino@yahoo.com


1. Allah gwani kai ne ka kagi samaniya,
Kai yo maza mata cikin su halitta.

2. Ka ce mu so Manzo Rasulu abin biya,
Da gun Aminatu Sidi ya cancanta.

3. Na san akwai so gaskiya ne ’yan’uwa,
Domin ko Rabbi ya sa shi nan ga halitta.

4. Me sa mutum ya zamo kamar wani jarumi,
Me ji kamar zai doke dukka halitta.

5. Da can ina zargi a kan mai so ku ji,
Na mai da shi wawa cikinsu halitta.

6.Yau ga shi na fada a tarko har wuya,
Bege a kan wata ’ya cikinsu halitta.

7. Kullum na zo barci in ta tararradi,
Domin tunanina yana a gare ta.

8. In don mafarki na yi sau zambar dubu,
Domin yawan shaukin in sami ganinta.

9. A cikin mafarki mun hade mun daddale,
Amma a fili babu wanda ya furta.

10. Kwayar idonta kawai tana rikitar da ni,
Balle ta yo farfar da na dube ta.

11. In tai fishi sannan take dada kyan gani,
Balle harara ta fi kyau a wurin ta.

12. Tsari da suffa ba batunsu a nan wurin,
Ta zarce duk wani kyau da za a musalta.

13. Hakuri damo ya sallama mata kun jiya,
A cikinsu mata ban ga wadda ta kai ta.

14. Ni na zamo sarki a harkar so ku san,
Amma a yau na zam mariri gun ta.

15. Ya zan yi ne na zamo gwani a wajen ta ni?
Har ma ta san ni ta san ina kaunarta.

16. Ni ba ni so na fada da baki ta san ina,
Mutukar masifar so yana a gare ta.

17. Babbar bukatata a ce ta san da ni,
Ta gane lallai ni ina begenta.

18. Ko da ko ba ta so gare ni ku tabbata,
Na cim ma burina a kan kaunarta.

19. Ya ’yan’uwa ku taho da tanyon agaji,
Ko na ji sau}i kan batun matsayinta.

20. Ya zan yi ne in warke ciwon nan kuwa,
In sami yarjewa cikin kalbinta.

21. Ciwo kadan da kadan yake dada karuwa,
Wata ran a wayi gari ya kai ka ka kwanta.

22. Ni shawara na bida gare ku mawallafa,
In bayyana ne ko ko kadda na furta.

23. ’Yan Dandali ku fito da amsar tambaya,
Ku malamai ne kan sa so ku fahimta.

24. In kun gaza kun ba mu kunya bai daya,
Sai dai na ce kaico a harkar son ta