Tuesday, December 16, 2008



SIRADIN RUBUTU

Daga

Nurudden Ado Gezawa salmannhur@yahoo.com
07028821493, 08077879218

Kamar yadda zukar kahon wanzamai kan zuko kwantaccen jini, haka yanayin da na kasance ciki na karance-karancen kirkira ya zuko kwantacciyar basirar kirkirar labarai a kwakwalwata. Basirar kirkirar da ta bani damar shusshuka irirrikan labaran da yabanyarsu ke kan ganiyarta ta habaka, wanda hakan ya sanyani zumudin yadda zan yi wajen sharer fagen samun karbuwar labaraina.
Kodayake dai furfura ta rinjayi baker suma a kaina amma ba ta tsufa ba ce, ballantana a ki jinjinawa hangen nesan da na yi wajen samarwa kaina suna na musamman a fagen rubuce-rubucen kirkira. Ba kuma zabar Kanon da na yi a matsayin garin da zai zamo sabon matsugunina, kasancewarta jigon hausa, ne abin jinjinawar ba, a’a, tunanin sifar da ta kyautu in je Kanon da ita ne.
Na sha jin ana cewa idan har kanawa na da rauni to bai huce na tsantsar kaunar Musulunci ba. Ko da yake dai ni ban yarda da wannan a matsayin rauni ba, illa iyaka dai mashigar da idan mutum kadangare ne to zai iya shiga bangon kanawa ta cikinta. Don kuwa, mutumin duk da kanawa suka lura mabiyin Allah ne kuma masoyin Manzon Allah ne, to take su ke karbarsa ba tare da bincikar ainihin hali ko asalinsa ba. Wannan ya sanya na tanadarwa kaina lakabi na musamman d azan shiga Kano da shi, wanda na tabbatar kanawa za su rinka kira na da shi cikin nishadi da karamci, wanda hakan n eke nuni da samun karbuwa gurin na kanawa. Matukar haka ta faru kuwa, to babu ko tantama zan cimma burina na samun karbuwa a ilahirin kasar Hausa.
A wata ranar lahdin farkon wani watan miladiyya da hantsi na shigo birnin na Kano cikin wata shudiyar baksuwajata, wadda na lilliketa da lakabin da na tanadarwa kan nawa, na biyo ta titin Gwarzo. Da yake ban san inda zan bi don zuwa dakin karatun Murtala Muhammed ba, inda nan ne ake taron kalubalen kungiyar marubuta rishen jihar Kano, sai na dakata a wani guri, da a gaba, zan san sunansa a matsayin Sabon-titi don yin tambaya. Tun kafin ma na fita daga motar mutane suka rinka tunkaro motar a guje, suna yin kabbara. Raina ya yi fari bisa ga zaton da na yin a cewa na shigo da kafar dama fiye da yadda na zata.
Amma ba haka al’amarin ya tafi ba, don kuwa mutanen na karasowa sai suka rinka lalubar makamai suna jibgar motar tawa. Kafin ma na ankara sun rotes gilasan motar, sun zaro ni daga cikin motar sun kuma fara yi mini rajamu.
Lokaci na gaba da na farfado sai na tsinci kaina cikin bandeji, a gurin dab a tare da bata lokaci ba na shaida asibiti ne. Haka na yi ta fama har zuwa lokacin da ma’aikaciyar jinyar ta lura dani, inda bad a jimawa ba babban likita, tare da wasu mutane suka zo gare ni.. Bayan da likitan ya duba jikina sai ya waiwayi daya daga cikin mutanen, wanda kayan dake jikinsa ke nuni da cewa shi dansanda ne, ya ce masa ‘Bismillah’
Dansandan ya yi mini wasu tambayoyi, na kuma amsa masa. Tambayar da ta fi bani mamaki ita ce wadda ya ce “Da ka san Kanon garin Musulmai ne mai ya sanya ka yi wa Musuluncin wargi?”
Kaina ya daure “Yi wa Musulunci wargi? Ban gane ba.”
Ya ce “To mai ka rurrubuta a jikin motarka?”
Na ce “Lakabin da na ke son mutanen Kano su sanni da shi.”
Ya dan nazarce ni kafin ya ce, “Za ka iya gaya mini lakabin da kake son Kanawan su sanka da shin?”
“Kwarai kuwa,” na shaida masa, “Ba wanda ya gagari Allah.”
Dansandan ya karangai da kai cikin jimami, “To ai kai ba haka ka rubuta ba. Abin da ka rubuta shine Bawan da ya gagari Allah.”
Sai a sannan na gane dalilin dukan da aka yi mini, wanda ya faru ta sanadiyyar rashin bin ka’idojin rubutu! Hakika na rubuta ‘Bawan da’ a maimakon ‘Ba wanda’ wanda hakan ya jirkita manufata. Lallai ka’idojin rubutu su ne siradinsa, kuma rashin binsu kan iya janyowa mutum rasa, ko da, ransa. Don haka wajibi ne bayan basirar rubutu ga marubuci, ya kyautu ya sani ya kuma kiyaye dokokin rubutu cikin rubutunsa.